Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa, a rangadin da manzon musamman na Amurka kuma mataimakin sakatariyar harkokin wajen kasar kan gabas ta tsakiya ke yi a yankin, a jiya ya gana da wasu daga cikin jagorin addinai a kasar labanan, da suka hada jagorin mabiya mazhabar shi'a da kuma wasu jagororin ahlusunna da kuma jagororin mabiya addinin kirista, gami da wasu kungiyoyin siyasa.
Ziyarar tasa a Labanan ta z one bayan kammala ziyararsa a kasar Syria, inda ya gana da ministan harkokin wajen Walid Mu'allim dangane da wasu batutuwa, duk da dacewa har yanzu manzon musamman na Amurka bai bayyana takamaimai abin da suka tattauna tare da jami'an kasar Syria ba, amma dai ya tabbatar da cewa tattaunawar tasu ta yi armashi.
374806