IQNA

Hadin Kan Musulmi Shi Ne Hanyar Bijire Wa Hukuncin Kotun Duniya Kan Albashir

16:18 - March 10, 2009
Lambar Labari: 1754309
Bangaren Siyasa: Hukuncin da kotun manyan laifuka ta duniya ta fitar kan shugaban kasar Sudan Umar Albashir, babban cin fuska ne ga al'ummar kasar Sudan.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da limamin birnin Biranshahr da ke cikin lardin Azarbaijan ta gabas (Mostafa Mahmudi) ya bayyana cewa; hukuncin da kotun manyan laifuka ta duniya ta fitar kan shugaban kasar Sudan Umar albashir, babban cin fuska ne ga al'ummar Sudan baki daya da ma musulmi, kuma hakan ya tabbatar da cewa hadin kai tsakanin musulmi shi kadai hanyar kalubalantar zalunci da danniya ta kasashen yammacin turai, wadanda suke amfani da kotun duniya wajen cimma manufofinsu na siyasa.
Ya kara da cewa; hukuncin na kotun duniya kan shugaban Sudan bai ginu kan adalci na nashari'a ba, illa manufa ta siyasa.

375265


captcha