A wata hira da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna Mas'ud Karimi mahardacin kur'ani na kasa da kasa ya bayyana cewa idan ana maganar karatun kur'ani da iya harda dalla-dalla ba za a fice malam Mustapha Isma'il ba kuma dole a jinjina masa da daga masa tuta.Kuma ya san harshen larabci da hakan ma ya kara taimaka masa wajen fitar da harufa da salo mai kyau ta wannan fanni na karatun kur'ani mai tsarki da daukaka.
373771