Bayan ta nakalto daga majiyar Islam Online ,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Sheikh Imam Kingamba masani kan mazhabobin musulunci kuma mamba a komitin shirya bukukuwan Maulidin Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata a gare shi da alayan gidansa ya bayyana cewa: sun aika goran gayyata ne ga kiristoci a fadin kasar inda suka bukace su da su zo su taya su murnar wannan rana mai albarka ta tunwa da ranar haifuwar manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi kuma suka amsa wannan gayyata ta musulmi da hannu bibiyu da burin Karin fahimtar wannan addini na musulunci.wannan babban lamari ne na ci gaba wajen tabbatar da sulhu da hadin kai.
375904