Cibiyar da ke kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ce ta kawo labarin wannan ganawa mai matukar muhimmanci da armashi tsakanin jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatullahi Ali Khamna'I da kuma wakilan da suka halarci wannan taro karo na ashirin da biyu da suka fito daga kasashe sama da 150 dauke da matsalolin da ke addabar kasashen musulmi da kuma hanyoyin bi wajen magance wannan matsala. Jagoran ya bada shawarri da za su taimaka wa musulmi wajen magance sabanin da ke tsakaninsu matukar sun yi aiki da su da kuma muhimmancin da hadin kai a tsakanin musulmi ke da shi a yau musamman a wannan lokaci da musulmi ke fuskantar takurawa da nuna masu karan tsana a duniya.
378036