Bayan ta nakalto daga ofishin da ke hulda da jama'a a kotun kolin jamhuriyar musulunci a Iran ,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Ayatul Said Mahmud Hashimi Shahrudi shugaban kotun kolin jamhuriyar musulunci ta Iran a lokacin da yake ganawa da shugabannin yankin loristan ya yi masu barka da sallar maulidi ta tunawa da ranar haifuwar fiyayyan halitta muhammadu dan Abdullahi (SWA) da kuma jikansa Imam Sadik (AS) ya bayyana wannan raneku masu muhimmanci ga al'ummar Iran kuma musulmi musamman Iraniya sun taumaka wajen yadawa da daukakar musulunci a yau.
378018