Bnagaren kasa da kasa: Kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya gudanar da wani zama a ranar Alhamis da ta gabata, inda ya amince da daftarin kudiri da kasashen musulmi suka mika masa da ke neman ya haramta cin zarafin addinai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa; kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya gudanar da wani zama a ranar Alhamis da ta gabata, inda ya amince da daftarin kudiri da kasashen musulmi suka mika masa da ke neman ya haramta cin zarafin addinai. Kasashen musulmi sun wakilta kasar kasar Pakistan wadda mamba ce a kwamitin da ta mika daftarin kudirin ga kwamitin, wanda ya samu amincewar kasashe 23 daga cikin kasashe 34 mambobi kwamitin, yayin da kasashe 11 daga cikin mambobin kwamitin suka ki amincewa da shi, kashen turai da ke kwamitin ne suka ki amincewa da wannan daftarin kudirin, bisa hujjar cewa ya yi hannun riga da 'ynacin fadar albarkacin baki.
380564