Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; babban malamin addinin Musulunci na kasar Kirgistan ya bayyana cewa daga yau Asabar za a fara tattara taimakon jama'a domin gina babban masallacin juma'a a birnin Bishkek fadar mulkin kasar. Babban malamamin (Morad Ali Haji Jumanuv) ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar yau a birnin Bishkek fadar mulkin kasar, wanda ya samu halartar dubban musulmin kasar, ya ce babban abin alfahari ne ga al'ummar musulmin kasar su gina babban masallaci wanda zai zama shi ne mafi girma a kasar domin gudanar da tarukan addini. Ya ce aikin ginin masallacin zai lakume kudi har dalar Amurka miliyan 4, amma ya zuwa yanzu mutane sun yi tara kimanin kashi 40 cikin dari na wadannan kudade, kuma da yardar Allah za a fara gini.
380513