IQNA

Haramtacciyar Kasar Isra'ila Na Fakewa Da Rikicin Cikin Gida Na Palasdinu

15:30 - March 29, 2009
Lambar Labari: 1758717
Bangaren siyasa da zamantakewa: Sheikh Afif Nablis shugaban komitin malummai a jablul Amil a kasar Labanon ya yi nuni da tabarbaerewar tsaro a Labanon da Palasdinu da kuma fitinar rikicin cikin gida da yadda ke amfanar makiya.
Daga Labanon ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa labarin cewa; Nablis ya kara da cewa: haddasa rikici da sabani gami da rashin fahimtar juna a cikin gida a Labanon da Palasdinu ba kowa zai amfana ba sai makiya da hakan ked a babban hadari a tsakanin rayuwarsu da kuma makomarsu a nan gaba. Ya kara da cewa: Haramtacciyar kasar Isra'ila it ace ke bin hanyoyin haddasa wannan rikici da fitina ta cikin gida a Labanon da Palasdinu domin ta haka ne wato ta bin hanyoyin abukkanta na cikin gida za ta cimma burinta da ta jima tana son ganin ta isa a gare shi ta kowa ce hanya da salo.

381028

captcha