IQNA

A Karon Farko An Fassara Wasu Ayoyin Kur'ani A Cikin Yaren Hindiku A Pakistan

15:46 - March 30, 2009
Lambar Labari: 1759014
Bangaren kasa da kasa: A karon farko an fassara wasu ayoyin kur'ani da yaren Hindiku a Pakistan.
Bayan ta nakalto daga jaridar News ,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Abdul Gafur Malik ne ya fassara wasu ayoyin a cikin wannan yare na kasar Pkistan kuma ya share shekaru goma sha shidda ya yi yana fassara da kuma ya kawo karshen wannan fassara a shekara ta 2004 har ila yau kuma a karon farko hukumar da ke kula da al'adu da zamantakewa da adabi ta yaren Hindiku ce ta umarci yin hakan. Wannan littafi yanada shafi 1234 inda asalin ayoyin ke cikin harshen Larabci sai kuma fassara a gefe daya.

381347
captcha