IQNA

Akwai Yuwuwar Iran Sake Yin Nazari Kan Dangantakarta Da Masu Kare Ta'addanci

14:18 - April 05, 2009
Lambar Labari: 1760545
Bangaren kasa da kasa: Kwamitin kula da harkokin tsaron kasa a majalisar shawara ta Iran ya yi dubi kan batun sake yin nazari dangane da ci gaban alakar Iran ta fuskacin tattalin arziki tare da kasashe masu girman kai da ke kare ta'addanci a duniya.
Kmafanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; kwamitin kula da harkokin tsaron kasa a majalisar shawara ta Iran ya yi dubi kan batun sake yin nazari dangane da ci gaban alakar Iran ta fuskacin tattalin arziki tare da kasashe masu girman kai da ke kare ta'addanci a duniya. Bangaren hulda da jama'a na majalisar shawara ta kasar Iran ya sanar cewa, a karshen makon nan ne majalisar za ta duba batun wanda kwamitin kula da harkokin tsaron kasa na majalisar ya tattauna kansa, dangane da batun yuwuwar ci gaba da danganta tsakanin Iran da kuma kasashe masu kare ta'addancin Haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar musulmi ko kuma dakatar da dangantakar baki daya. Amma a cewar jami'in da ke kula da wannan bangare za a dauki mataki ne kan hakan bayan tattaunawar dukkanin wakilan majalisa.



382494
captcha