IQNA

An Fara Taron Kasa Da Kasa Kan Fikhu A Kasar Oman

16:07 - April 06, 2009
Lambar Labari: 1761115
Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da zaman taro kan fikun musulunci a birnin Maskat na kasar Oman.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (islam online) cewa; A ranar Asabar da ta gabata ce aka fara gudanar da zaman taro kan hukunce-hukuncen musulunci da ke cikin littafan fikhu, wanda ke samun halartar malaman addini da kuma masana daga kasashe 14, inda suke yin bahasi kan makomar wasu daga cikin hukunce-hukuncen fikhu da kuma yadda za a yi aiki da su a nan gaba, bisa la'akari da canje-canjen da ake samu a cikin rayuwa ta zamani. Manyan malamai gami dam asana daga jami'oi daban-daban sun gabatar da makaloli 36 a wajen zaman taron, inda suka bayyana mahangarsu kan hukunce-hukunce tare da la'akari canje-canjen rayuwar zamani, inda suka jaddada wajabcin la'akari da irin wadannan canje-canjen da ake samu da kuma bambancin al'ummomi wajen aiwatar da wasu hukunce-hukuncen. Za a kwashe kwanaki hudu ana gudanar da wannan zaman taro a birnin Mskat.


382922


captcha