IQNA

Al'ummar Duniya Na Goyan Bayan Aiwatar da Dokoki An Abin Da Ya Faru Kan Zirin Gaza

16:01 - April 06, 2009
Lambar Labari: 1761132
Bangaren kasa da kasa: al'ummar duniya na goyan bayan ganin an aiwatar da adalci da dokoki kana bin day a faru kan zirin gaza na zalumcin Haramtacciyar kasar Isra'ila.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Ma'an ta watsa labarin cewa: shugaban hukumar kula day an gudun hijira a Palasdinu da ke karkashin majalisar dinkin duniya Jan Ging ya bayyana cewa: idan al'ummar duniya suka goyi bayan aiwatar da dokokin kasa da kasa kana bin day a faru na zalumci a Gaza to yanayi a yankin zai yi kyau da daidaita.Har ila yau ya kara da cewa: yanayin da al'ummar yankin Gaza ke ciki ya yi muni matuka gaya hatta bas u iya ciyar da kawunansu da magance bukatunsu nay au da kullum kuma yau kusan watnni biyu da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaiwa Gaza hari amma har yanzu yanayin al'umma ya yi muni.

383026

captcha