Bayan ta nakalto da majiyar labarai a majalisar dokoki ta Iran ,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa:Hashmatullah Falahat Pisha mamba a komitin tsaro ada siyasar harkokin waje a majalisa a matsayinsa na shugaban tawagar Iran a wajen taron hadin gwiwar majalisun dokokin duniya ya bayyana cewa: yau shekaru da dama duniya na fama da rikice-rikice na rashin adalci kuma a kullum sai lamarin kara muni yake yi. Kuma Ya kara da cewa yanayin da ake ciki a yau lamarin sai kara muni yake yin a nuna danniya da zalunci a fili .har ila yau ya ci gaba da cewa matukar ba a dauki mataki ba cikin gaggawa to ba a san abin da zai faru a nan gaba ba domin babu wani hakki da ake karewa ko ake kiyaye wa musamman na marassa karfi da su ne suka fi fama da wannan matsala a fili karara.
383737