IQNA

An Kirayi Duniyar Musulmi Zuwa Ga Kare Masallacin Qods

16:51 - April 12, 2009
Lambar Labari: 1763841
Bangaren kasa da kasa; A daidai lokacin da shisshigin yahudawan sahyuniya ke ta karuwa kan al'ummar Palastinu da kuma masallacin Qods mai alfarma ke ta karuwa, limamin masallacin Qods din ya kirayi dukkanin musulmin duniya da larabawa zuwa ga kare masallacin Qods da alfarmarsa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (NASIJ) cewa; limamin masallacin Qods din ya kirayi dukkanin musulmin duniya da larabawa zuwa ga kare masallacin Qods da alfarmarsa. Wannan kira na limamin masallacin Qods ya zo ne a daidai lokacin shishigin yahudawan sahyuniya kan masallacin Qods da ma al'ummar Palstinu ga baki daya ke ta karuwa, limamin ya ce wadannan matakai da yahudawan ke dauka matakai ne na aiwatar da shirinsu na mayar da birnin Qods baki dayansa mallakin yahudawa, tare da rushe masallacin kowa ya rasa, inda yanzu haka suke ci gaba da fafare karkashinsa, ya ce wajibi ne da ya rataya kan al'ummar musulmi ta duniya da su kare masallacin Qods, domin kuwa a cewarsa dukkanin wuraren musulunci masu tsarki amanar ubangiji ce ga musulmi, kuma wajibi na shari'a su kare wannan amanar kamar yadda Allah ya dora ta kansu. Haka nan kuma wajibi ne ga musulmi su taimaki 'yan uwansu musulmi da ke Palastinu da ke fuskantar danniya da zalunci daga yahudawan sahyuniya.

386091



captcha