Cibiyar da ke kula harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; Hasan Salahi shugaban ofishin da ke kula da yada addinin musulunci a Sabe a ranar litinin da ta gabata a taron farko a wannan shekara da ak gudanar da taron ofishin tare da ma'aikata masu kula da yadda ake yada addini ainda ya bayyana cewa: ana bukatar canja dokoki idan ana son a tabbatar da wannan manufa a aikace kuma kowa ya ji dadin rayuwa cikin sauki da walwala kuma babu almubazziranci a ciki. Ya kara da cewa; kamar sauran guraren watsa labarai suma jami'o'I za su taka rawar gani a wannan fanni na hana almubazziranci a aikace.
386740