IQNA

An Bude Taro Kan Mahangar Imam Khomeini Dangane Da Juiyin Juya Hali

22:17 - April 16, 2009
Lambar Labari: 1765737
Bangaren siyasa da zamantakewa: An bude taro a jami'ar mazhabobin musulunci da ke birnin Tehran, domin yin nazari dangane da mahangar Imam Khomeini kan juyin juya halin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren kula da taruka na jami'ar mazhabobin musulunci da ke Iran cewa; : an bude taro a jami'ar mazhabobin musulunci da ke birnin Tehran, domin yin nazari dangane da mahangar Imam Khomeini kan juyin juya halin muslunci, wanda kuma taron na hadin gwiwa ne tsakanin jami'ar da kuma ma'aikatar ilimi. Bayanin ya ci gaba da cewa a wajen taron an yin sharhi ne kan wasu littafai ko laccoci na Imam da suka shafi juyin juya halin musulunci, inda a kan bayyana mahangar Imam tare da yin sharhi kan hakan. Taron dai yana samun halartar masana daga sassa daban-daban na kasar Iran gami da daliban jami'a da suka rubuta makaloli kan hakan.

389082




captcha