IQNA

Cibiyar Fikihun Musulunci Ta Ja Kunnen Isra'ila Kan Keta Alfarmar Qods

15:49 - April 20, 2009
Lambar Labari: 1766517
Bangaren kasa da kasa: Cibiyar kula ayyukan fikihun Musulunci ta ja kunnen Isra'ila dangane da duk wani mataki na barazanar keta alfarmar masallacin Qods da yahudawa masu tsatsauran ka iya dauka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-riyad) da ake bugawa a kasar saudiya cewa; cibiyar kula ayyukan fikihun Musulunci ta ja kunnen Isra'ila dangane da duk wani mataki na barazanar keta alfarmar masallacin Qods da yahudawa masu tsatsauran ka iya dauka. Cibiyar ta sanar da hakan ne a cikin wani bayani da ta fitar jiya, inda ta bayyana cewa yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi na ci gaba da yin barazanar afka wa masallacin Qods mai alfarma, tare keta lafamarsa da ma daukar matakan rusa shi domin kowa ya rasa, bayanin ya ce dukkanin abin wadannan yahudawa ke yin a ci zarafin palastinawa da ke Qods da yunkurin keta alfarmar masallacin mai tsarki, hakan na samu daurin gindi ne daga gwamnatin Isra'ila, a kan haka dole gwamnatin yahudawan ta kawo karshen haka.


390152

captcha