Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (KUNA) na kasar Kuwait cewa; kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta bukaci kasashen duniya da su taka rawa wajen taka wa Isra'ila birki kan ayyukan wuce gonad a iri da take aikatawa kan al'ummar palastinu da suka yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa. Daraktan bangaren da ke kula da kare hakkin dan adam na kungiyar hadin kan kasashen larabawa Mahmud Arshad shi ne ya bayyana hakan a jiya, inda ya ce cin zarafin al'ummar palastinu mazauna birnin Qods da keta alfarmar masallaci gami da dukkanin alamu na musulunci da yahudawan sahyuniya suke yi ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa, ya ce wajibi ne da ya rataya kan al'ummomin duniya da su taka wa yahudawa birki kan wannan ta'asa da suke tafkawa.
390012