IQNA

An Bude Filin Rubuta Sunaye Ga Duk Mai Son Shiga Gasar Karatun Kur'ani Na Sarki Kabus Na Oman

16:04 - April 18, 2009
Lambar Labari: 1766531
Bangaren kasa da kasa: cibiyar kula da al'adun musulunci ta Sarki kabus ta fara karba da rubuta sunayen duk wanda yake son shiga gasar karatun kur'ani a sarkin kasar ta Oman.
Bayan da jaridar Alshaiba da ake bugawa a kasar Oman ta kawo labarin ,cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ta watsa labarain cewa;cibiyar da ke kula kula da yada al'adun musulunci ta sarki Kabus na kasar Oman ta fara karbar sunayen duk wanda yake son shiga da damawa da shi a cikin gasar karatun kur'ani a wannan kasa.Sai dai wani hamzari ba gudu ba duk wanda ya kasance bai taba cin wata lambar yabo ta karatun kur'ani ta kasa da kasa ba shi da damar shiga wannan gasa .Wannan yana daga cikin sharadin babban da wannan kasa ta yi gindaya ga duk wanda yak e son shiga wannan gasa.

389123
captcha