IQNA

An Bude Makarantar Koyon Koyon Ilmomin Kur'ani A Palastinu

16:32 - April 20, 2009
Lambar Labari: 1767585
Bangaren kasa da kasa: An bude makarantar koyon ilmomin kur'ani a sansanin palastinawa 'yan gudun hijira na Majdul karum da ke arewa maso gabacin palastinu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na bokrat.net cewa; an bude makarantar koyon ilmomin kur'ani a sansanin palastinawa 'yan gudun hijira na Majdul karum da ke arewa maso gabacin palastinu. A yayin bude makarantar malamai dam asana sun halarci bukin budewar, daga cikinsu kuwa har da manyan daraktocin makarantu na palastinu, tare da hadin gwiwa tsakanin makarantar da kuma cibiyar kula da harkokin ilimi ta palastinu. An saka ma makarantar sunan wani matashi bapalastine Amir Mahmud Khayila wanda ya ya yi shahada a sansanin a cikin shekarar da ta gabata, bayan da sojojin yahudawan sahyuniya suka kai wani farmaki a yankin.

390840


captcha