Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto daga bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Hasan Kashkawi na bayyana cewa ya kamata kasar Masar ta fahimcin irin barazanar da ke fuskantar kasashen musulmi a yau daga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.Kuma ya zama dole kuma wajibi gwamnatin kasar Masar ta daidaita harkokinta da sauran kasashen musulmi a maimakon ta ci gaba da zarginsu a kai akai da yi wa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila hidima babu ji babu gani da hana isar da duk wani taimako zuwa ga yan uwansu musulmi kuma larabawa a yankin gaza.
391451