Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran SANA cewa; A wani taron masana tarihi da aka gudanar a sansanin palastinawa 'yan gudun hijira da ke yarmuk, mataimakin hadaddiyar kungiyar larabawa masana tarihi Suhail Zakhan ya bayyana cewa; Yahudawan sahyuniya na duniya na yin amfani da kafofin yada labarai na kasashen yammacin turai wajen yada mummunar manufarsu da tunaninsu kan masallacin Qods mai alfarma da ma birnin baki daya. Ya ci gaba da cewayahudawan sahyuniya suna da wata akida ta musamman dangane da Qods, inda suke ganin cewa larabawa da musulmi ba su da wata dangantaka birnin Qods balantana masallacin Qods mai alfarma, kuma dole ne su kautar da hankulan al'ummomin duniya dangane da tarihi, wanda yake danganta musulmi da larabawa da masallacin Qods, kuma yanzu haka yahudawan suna yin amfani da kafofin uada labaran kasashen yammacin turai ne wajen yada wannan manufa.
393493