Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP cewa; Manyan jagororin fadar Vatican tare da kungiyar hadin kan kasashen larabawa sun rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi na yin aiki tare a bangaren siyasa da al'adu. Ministan harkokin fadar Vatican tare da sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa Amr Musa ne suka rattaba hannu kan yarjejeniya, bisa fatan ganin hakan ya taimaka wajen kara samun fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu, tare da kara tabbatar tsaro a yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda hakan ake fatan zai kara dankon alaka ta fuskacin siyasa da al'adu tsakanin larabawa da kuma sauran mabiya addinin kirista. A nasa bangaren Amr Musa ya bayyana cewa nan bad a jimawa ba zai gana da jagoran fadar Vatican paparoma Benedict na goma sha shida.
393526