IQNA

Bangaren kasa da kasa: Za a gina jami'ar musulunci a kasar Senegal bisa kokarin da ma'aikatar kula harkokin ilimi mai zurfi ta kasar Segal take yi tare da taimakon kasar saudiyya.

15:15 - April 25, 2009
Lambar Labari: 1769246
Bangaren kasa da kasa: Za a gina jami'ar musulunci a kasar Senegal bisa kokarin da ma'aikatar kula harkokin ilimi mai zurfi ta kasar Segal take yi tare da taimakon kasar saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran APS cewa, ministan ma'aikatar kula da harkokin ilimi mai zurfi na kasar Senegal Mostapha Sourang ya bayyana cewa; za a gina jami'ar ne a garin Dianiadio, kamar yadda za a gina wata makarantar sakandare ta musulunci a Keur Massar da ke kusa da birnin Dakar fadar mulkin kasar. Ya ce ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Saudiya tare da hadin gwiwar ma'aikatar kula da harkokin ilimi mai zurfi ta kasar Senegal za su gudanar da aikin tare, kuma yanzu haka bangarorin biyu sun fara gudanar da aikin kamar yadda aka tsara.

393551

captcha