IQNA

Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam Sun Soki Isra'ila Kan Rahoton Yakin Gaza

15:16 - April 25, 2009
Lambar Labari: 1769370
Bangaren kasa da kasa: Kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya na ci gaba da yin kakkausar suka, dangane da rahoton da Isra'ila ta bayar kan binciken da ta ce ta gudanar kan yakin Gaza, inda ta wanke sojojinta daga aikata aikata laifukan yaki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya naklato daga shafin internet na Islam online cewa; Da dama daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya na ci gaba da yin kakkausar suka, dangane da rahoton da Isra'ila ta bayar kan binciken da ta ce ta gudanar kan yakin Gaza, inda ta wanke sojojinta daga aikata aikata laifukan yaki. A cikin wani bayani da mataimakin shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa ya fitar, ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a cikin rahoton da Isra'ila ta fitar dangane day akin Gaza, inda ta sa sabulu ta wanke sojojinta daga aikata laifukan yaki da ake zrginsu da aikatawa kan fararen hular Gaza. Ya ce abin da ya faru a kan idanun al'ummomin duniya ya faru, saboda haka Isra'ila na kokarin yin yawo da hankulansu ne, kuma hakan ba zai hana ci gaba da bin matakan da suka d ace ba, domin gudanar da sahihin bincike.

393655


captcha