IQNA

An Bayyana Sunayen Wadanda Za Su Shiga Gasar Kur'ani Ta Amir Salman

15:16 - April 25, 2009
Lambar Labari: 1769373
Bangaren kasa da kasa: Ya zuwa yanzu adadin wadanda aka sanar da sunayensu daga cikin wadanda za su shiga gasar kur'ani ta Amir Salman a birnin Riyad na kasar Saudiya, ya kai yara maza da mata 91, inda za a gudanar da gasar kasa da makonni biyun masu zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Aljazeera da ake bugawa a kasar Saudiiya cewa; ya zuwa yanzu adadin wadanda aka sanar da sunayensu daga cikin wadanda za su shiga gasar kur'ani ta Amir Salman a birnin Riyad na kasar Saudiya, ya kai yara maza da mata 91, inda za a gudanar da gasar kasa da makonni biyun masu zuwa. Babban daraktan ma'aikatar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar saudiyya Abdulaziz bin Abdulrahman ya bayyana cewa; tun shekaru 11 da suka gabata ne aka fara gudanar da gasar hardar kur'ani ta kanan yara a kasar Saudiyya, amma wannan shi ne karon farko da yarima Sultan ya shirya gudanar da gasar wadda zai dauki nauyinta, wadda za a gudanar tsawon kwanaki 10 a babban oten din nan na Idihar Holiday da ke birnin Riyad.

393668




captcha