IQNA

Jagoran Juyin Juya Hali Ya Mika Sakon Ta'aziyyar Shahidan Kazimiyya

17:13 - April 26, 2009
Lambar Labari: 1770091
Bnagaren siyasa: jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka yi shahada sakamakon harin ta'addancin da aka kai kansu yayin ziyarar wurare masu tsarki a Iraki, inda ya bayyana cewa sojojin mamayar Amurka sun e ummul haba'isin hakan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ofishin jagoran juyin juya halin musulunci a Iran cewa; Ayatollah Osma Sayyid Ali Khamenie jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka yi shahada sakamakon harin ta'addancin da aka kai kansu yayin ziyarar wurare masu tsarki a Iraki, inda ya bayyana cewa sojojin mamayar Amurka sun e ummul haba'isin hakan. Bayainin ta'aziyar ya zo kama haka: Da Sunan Allah mai rahama mai jin kai. Abin day a faru na kai hari kan masu ziyartar wurare masu tsarki a kasar Iraki masu neman yardarm shedan ne, wadanda ba su san wani abu 'yan adamtaka ba. Babban ummul haba'isin haka kuwa ba kowa ba ne illa dakarun mamayar Amurka da ke Iraki, wadanda da sunan yaki da ta'addanci suke aikata ta'addanci a kasar musulmi. Abin da muke jira daga gwamnatin Iraki shi net a dauki matakan da suka kamata domin kalubalantar irin wadannan ayyukan ta'addanci. Muna rokon Allah mai rahma da jinkai, da ya rahshe da wadanda suka yi shahada, ya kuma ba wadanda suka samu raunuka sauki.
Sayyid Ali Khamenei


394045
captcha