IQNA

Hizbullah Ta Soki Majalisar Dinkin Duniya Kan Laifukan da Isra'ila Take Tafkawa

14:01 - April 27, 2009
Lambar Labari: 1770585
Bangaren siyasa da zamantakewa: Wakilin kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah a kasar Labanan a kasar Labanan ya bayyana cewa, babu wani mataki da Majalisar dinkin Duniya ta dauka na takawa Isra'ila birki kan ayyukan yaki da take aikatawa, maimakon haka ma sai nuna halin ko in kula take yi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Labanan ya habarta cewa; Wakilin kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah a kasar Labanan a kasar Labanan ya bayyana cewa, babu wani mataki da Majalisar dinkin Duniya ta dauka na takawa Isra'ila birki kan ayyukan yaki da take aikatawa, maimakon haka ma sai nuna halin ko in kula take yi. Wakilin kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanan hassan Fadlollah ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a kudancin birnin Beirut, inda ya ce kasa daukar kwararn matakai da majalisar dinkin duniya ta yi kan Ira'ila ya tabbatar da raunin majalisar, kuma bai kamata a dogara da ita ba, kuma a cewarsa wani abin ban takaici shi ne yadda majalisar dinkin duniya ta zama ita ce mai kare Isra'ila da laifukan da take aikatawa ta hanyar fitar da kudurori ko furucin jami'anta.

394755


captcha