Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na musamman amma wannan karo za mu yi Magana ne kan zagayowar irin wannan rana da aka haifi Hadarat Zainab (AS) matar da ta samu matsayi da daukaka da kyawawan halaye kuma litattafan tarihi musulunci ya cika da bayaninta da rawar da ta taka a bangarori daban-daban na rayuwa saboda zagayowar wannan rana ta farin ciki ta haifuwar Hazarat Zainab (AS) nuna taya dukan musulmin duniya murnar wannan rana.
Ita dai Hadarat Zainab (AS) an haife ta ne a ranar biyar ga watan Jumada Awwal shekara ta shidda hijira kamariya a birnin Madina kuma ita ce diya ta uku daga cikin yayan imam Ali (AS) da fatimatuzzahra (AS) . Lokacin da Zainab (S) ta bude ido a wannan duniya Manzon Allah tsira da amincin Allah Ya Tabbata a gare shi da alayan gidansa yana cikin bulaguro,saboda haka sai ma'aifiyarta Fatima diyar manzon Allah (AS) ta bukaci mijinta imam Ali (AS) da ya sanyawa wannan diya tasu suna. Amma imam Ali (AS) ya jinkirta wannan lamari har sai manzon Allah ,manzon rahama Muhammadu dan Abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi ya komo daga bulaguro. Lokacin da Manzon Rahama (SWA) ya komo daga bulaguron da ya tafi ya nuna farin cikinsa matuka gaya da wannan jika tasa abin faranta masa da rai da bayyana cewa: Allah madaukakin sarki yana cewa: sunan wannan yarinya Zainab da ke nufin haske ko tauraron ma'aifi.Manzon Allah (SWA) ya dauke ta yana sinbatarta yana cewa ina umurtar ku da ku girmama wannan yarinya kuma ita ma tamkar Khadiza ce. Tarihi ya shaida gaskiya hakan cewa Zainab (S) tamkar Khadija ce wajen yadawa da taimakawa wajen kafuwar musulunci da daukakarsa kuma ta jurewa tsanani da wahalhalu masu yawan gasket kuma ta nuna tsayin daka da sadaukar da kai bugu da kari ta taka rawar gain wajen yada addini da ilmantar da shi ga jama'a.
Zainab (S) ta rayu ne a gidan tsarki da nubuwa da kuma karamci domin a wannan gida ne akwai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayan gidansa wanda aka yi duniya da lahira don shi kuma wannan shi ne fiyayyan wanda yafi kowa kyawawan dabi'u kuma a wannan gida ne imama Ali (AS) yake da kuma Fatimatul Zahra (AS) wadanda sune murhun tsarki da daukakar dan adam . Hadarat Zainab (S) tun tana karamar yarinya take da zurfin tunani da fahimta da ruhi na ma'anawiya.Hadazarat Zainab (S) tun tana karama take bada tarihin rayuwar ma'aifiyarta Hadarat Fatima Albatula (AS) da hakan ya bayyana dinbin ilimi da hazakarta ta ilimi da fahimtar addini da abubuwa na ma'anawiya kuma tana daga cikin masu kawo ruwayoyi da bayyana hakikanin abubuwan da suka faru a tarihi kuma hakan ya sa lokacin da ta girma saboda zurfin ilimi da fahimtarta ake yi mata lakabi da Akila da wannan suna ko lakabi yake nufin mace mai zurfi da karfin fahimta da dogon tunani. Zainab (S) tun tana karat a fara dandana dacin rayuwa domin kuwa tun tana karama ce kakanta fiyayyan halitta manzon Allah Muhammadu dan abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka bayan haka bad a jimawa ba ta yi bankwana da ma'aifiyarta fiyayyar matan duniya Fatimatul Zahra (AS) diyar ma'aikin Allah .Wannan ya sa ma'aifinta imam Ali (AS) ya karbi dawainiya da kula da tarbiyarta da zama uwa kuma uba a lokaci guda da hakan ya taimaka mata matuka gaya wajen samun tarbiya da kulawa ta musamman da kuma ilmantar da ita .Hadarat Zainab (AS) ta ilmantar da yada al'adun musulunci dare da rana da kuma mata da dama suka karu da samun ilimi da tarbiya gami da fahimtar addinin musulunci ta hanyarta . A majalisarta ce take koyar da mata ilimin addini da tafsirin Kur'ani mai girma da Hadisan Manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da limaman gidansa tsarkaka.Hadarat Zainab (S) a birnin Madina da kuma wani gajeran lokaci a birnin Kufa ta koyar da ilmantar da al'umma addinin musulunci da sauran fannoni na ilimi da tarihi.
Lokacin da hadarat Zainab (S) ta isa aure ta yi aure da Abdallah bin Jafara dan baffanta kuma Abdallah yana daga cikin masu kudi da arziki a cikin larabawa a lokacinsa amma Zainab (S) bat a taba bawa rayuwa ta madda muhimmanci da kulawa a zahiri ko a zucci saboda yadda take da karfi na ma'anawiya mai zurfi da daukaka ga kuma tarbiya ta gari da ta koya daga gidan tsarki da shirriya ta hakika. Ta kasance tana cewa duk yanayin dad an adam ya shiga bai dace ba kuma bai kamata ba ya sha'afa da rayuwa ta ma'anawiya da rungumar rayuwar madda , wannan yana daga cikin dalilan day a sa ta kama hanya da tafarkin dan uwanta imam Huseini (AS) tafarkin raya addinin Allah da kakansa ma'aikin Allah ya zo da shi domin shiryar da bil adama da tabbatar da sulhu da nutsuwa ta hakika. Hadarat Zainab (S) lokacin da za ta yi auri Abdallah ta kafa sharadin cewa dukan lokuttan rayuwarta su kasance tare dad an uwanta imam Huseini (AS) sharadin da Abdallah ya amince da shi ga Zainab (AS) . Kuma wannan shi ne dalilin day a sa Zainab (S) ta kasance tare dad an uwanta lokacin tsayuwar karbala da fita daga birnin Madina zuwa yankin Karbala na fuskantar Yazid wanda ya kawo banna da canja akalar addinin Allah da tafarkin gaskiya da Annabin Allah (SWA) ya zo da shi domin shiryar da al,ummar duniya daga bata da tabewa duniya da lahira.
Babban fili da dandali ko dammar fahimtar kyawawan halaye da matsayin Hadarat Zainab (S) shi ne yin dubi da rawar da ta taka a lokacin Ashura tun daga birnin madina zuwa yankin Karbala da kuma bayan abubuwan bakin ciki da suka faru a wannan yankin a ranar Ashura da bayan ta komo birnin Madina da yadda ta fuskanci Yazidu da kuma yadda ta jurewa abubuwan takaici da huzuni na karshe day a mamaye zuriyar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah Su tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka. A daidai wannan lokaci Zainab (S) ta nuna juriyya da karfin ruhi da azama kuma ta kasance babu kamarta afili da dandalin Ashura bayan abin da ya wakana inda ta tunkari Yazidu da wakilansa kan mummunan aikin da suka aikata kuma ta nuna kusancinta da Allah da rungumar gaskiya da tunkarar karya da zalunci na karshe kuma ta kasance jaruma a tsakanin mazaje azzalumai.Wajen ibada da neman yardarm Allah zainab ta yi fice domin ambaton Allah da Salla suna kwatar mata da hankali da sa mata nucuwa kuma hasken shiriya daga Allah ya mamaye zucciyarta da hakan ya sa duk wani kumci da tsanani da damuwa a wannan duniya ba ya damunta kuma wani abu ne da bai taka kara ya karya ba . Kamar yadda masana halaryar dan adam suka bayyana bai kamata ba mutum lokacin da yake cikin fushi da tsananin farin ciki ya dauki mataki mai muhimmanci To haka Zainab (S) ta kasance a duk lokacin da tsanani ya mamaye ta bayan shahadar dan uwanta abin kaunarta imam Huseini (AS) cikin nutsuwa ta gabatar da wani jawabi day a tabbatar da matsayinta da daukakarta ta fuskar hakuri,Jarumtaka da kuma tawakkali ga Allah da ya mamaye zucciya da rayuwarta da kuma bayyana matsayinta a fili. Zainab duk da kasancewarta mace amma ta nuna jarumtaka da tsayin daka wajen bayyana matsayi da darajar Ahlul Baiti (AS) da kuma tabbatar da cewa Imam Huseini (AS) da sahabbansa ne suka yi nasara a filin daga na Karbala lokacin da suka tunkari zalunci da banna domin kuwa hakan ya maido da martabar addinin musulunci .
Bayanai da jawabin da Zainab (S) ta gabatar kan Yazidu da mummunan aikin day a aikata ya mamaye zukatan duk wanda ya saurari wannan jawabi ya kuma tausaya mata da kuma kowa ya fahimci bakin zaluncin da ya wakana a Karbala masu sauran imani suka kara tausaya mata ita kuwa a daidai wannan lokaci ta tuno da mahaifinta Imam Ali (AS) da a nan ma ta sake sawa mutanan da ke guri suka tuno da shi tamkar yana a raye tare da su . Bugu da kari tana kafa hujjjoji da ayoyin kur'ani wajen bayyana hakikanin lamurra kamar yadda ibn Kasir daya daga cikin manyan malumman larabawa wajen fasaha yake bayyanawa jawabanta ya yi tasiri a rayuwarsa inda cikin babbar murya yake cewa; zan sadaukar da raid a rayuwata da kuma duk wani abu mai kima da daraja a gare ni domin kin kasance fiyayyar mata a wannan lokaci kuma kin fito ne daga gida mafi girma da daukaka da zuriya ta gari kuma jawabanki ya tabbatar da zurriyar da kika fito Allah ya sakawa wannan gida da suka sadaukar da rayuwarsu wajen shiryar da al'ummar duniya.
Hadarat Zainab (S) ta jiyo daga ma'aifinta imam Ali (AS) cewa: Dan adam bay a iya gano hakikanin imani sai mutuman day a kasance yanada abubuwa guda uku na musamman .Masaniya kan Addini ,hakuri kan kumci, tafiyar da rayuwa kan alheri. To wannan abubuwa guda uku za a iya samunsu a tattare da Zainab kuma ta nuna tsayin daga da juriya da hakuri kan hanyar gaskiya da neman yardarm Allah kuma karkashin haka ne ma bakin ciki ya mamaye zucciyarta lokacin Ashura. Amma da ke yau ranar farin ciki ce ina taya dukan musulmin duniya murnar wannan rana ta Haifuwar Hadarat Zainab (S)da fatar Allah ya bam u karfin koyi da ita da kuma kasancewa a kullum karkashin tafarkin zurriyar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka amin da kuma wannan ne ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na gabatar da wannan shiri na musamman na ke cewa wassalam alaikum warahmatullahi wa barkatuhi.