IQNA

An Kama Wani Mai zane A Masar Kan zargin Cin Mutuncin Musulunci

13:40 - April 29, 2009
Lambar Labari: 1771639
Bangaren kasa da kasa: Yan Sanda a kasar Masar sun yi awangaba da wani mai zane zane kirista kan zargiin batanci ga abubuwa masu kima da daraja na musulunci.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; ta nakalto daga jaridar Alhayat da ake bugawa a birnin London cewa Jamal Id shugaban ofishin kare hakkin dan adam larabawa a wata hira da manema labarai y ace; Hani Nazir Aziz marubucin littafin Karzul Hub a jiya an yi awangaba da shi kan zargin cin zarafin abubuwa masu kima na musulunci .

396031


captcha