Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na CAIR cewa, babbar majalisar Musulmi Amurka ta kirayi shugabannin yahudawan Amurka da ke majami'ar yahudawa a jahar Florida da su da su yi Allawadai da cin zarafin addinin mususulunci da Geert Wilders ke yi. Majalisar Musulmin ta yi wannan kiran ne a cikin wani bayani da ta fitar jiya dangane da cin zarafin dad an majalisar nan na kasar Holland ke Geert Wilders ke yi kan addinin musulunci da musulmi, wanda hakan ya sabawa dukkanin ka'idoji da dokoki na kasa da kasa, a nasa bangaren shugab majalisar musulmi ta kasar Amurka a cikin wani bayani da ya gabatar a majami'ar yahudawan ya bayyana cewa, kun san cewa furucin da Wilders ke kan musulunci wanda shi ne keda mabiya marassa rinjaye a turai ba kalamai ba ne da za su kawo zaman lafiya.
396777