IQNA

An Gudanar Da Taro Kan Kusanto Da Fahimtar Juna Tsakanin Addinai

20:31 - April 30, 2009
Lambar Labari: 1772078
Bangaren kasa da kasa: An gudanar da wani taro na mabiya addinai da nufin kusanto da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban na duniya a birnin Doshambeh na kasar Tajikistan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Kazinform cewa; An gudanar da wani taro na mabiya addinai da nufin kusanto da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban na duniya a birnin Doshambeh na kasar Tajikistan. Ofishin jakadancin kasar Kazakistan da ke birnin Doshambe na kasar Takistan ne ya dauki nauyin shirya tare da gudanar da wannan taro, wanda ya samu halartar masana da malamai da kuma wakilan cibiyoyi gami da kungiyoyin addinai da ma wakilan bangarori daban-daban na gwamnati. A wurin taron an tattauna irin rawar da addinin musulunci yake takawa wajen wanzar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban.


396688


captcha