Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga majiyar Internet ta Islam Anline ta watsa rahoton cewa: ofishin hulda da jama'a da kula dad an adam a majalisar dinkin duniya ya fitar da wata sanarwa da a ciki yake cewa; dole shugabannin haramtaciyar kasar Isra'ila cikin gaggauwa su kawo karshen rusa gidajen Palasdinawa da ke zaune a birnin Baitul Makadusi .Sai dai abin dora ayar tambaya shi wannan ba shi ne karon farko da majalisar dinkin duniya ke fitar da irin wannan sanarwa ko wannan karo gwamnatin haramtaciyar kasar Isra'ila za ta saurari majalisar kuma mai ya sa majalisar bat a daukan matakin day a dace kan Haramtacciyar kasar Isra'ila kamar yadda ta ke dauka kan sauran kasashe musamman musulmai daga cikinsu.
398075