Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na islamonline cewa; Kungiyoyin yahudawan sahyuniya da ke Amurka sun nuna harzukarsu dangane da yadda wani malamin jami'a a Amurka ya bayyana kisan kare dangi da Isra'ila ta yi a kan al'ummar Gaza da Holocost. Professor Willim Robinson wanda shi kansa bayahude ne kuma malalamin jami'a a Amurka, a cikin watan janairun da ya gabata, a cikin wasu sakonni day a rika aike wa dalibansa ta hanyar email, ya sheda musu cewa kisan kare dangin da Isra'ila ta yi kan al'ummar gaza ya yi kama da holocost. Da dama daga cikin kungiyoyin yahudawan shayuniya da ke Amurka ba su ji dadin wadannan kalamai.
397641