IQNA

An Gudanar Da taro Tsakanin Senegal Da Mauritania Karkashin OIC

17:56 - May 04, 2009
Lambar Labari: 1773956
Bangaren kasa da kasa: Abdallah Wad shugaban kasar Senegal a lokacin da yake bude taro da yahada Senegal da Mauritania a matsayinsu na kasashen musulmi a karo na farko a birnin Dakar ya bayyana cewa; wannan zama wani babban canji ne na ci gaba a cikin kungiyar hadin kan kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran APS cewa; Shugaban kungiyar hadin kan kasashen musulmi na karba-karba, kuma shugaban kasar Senegal Abdallah Wad a lokacin da yake bude taro da yahada Senegal da Mauritania a matsayinsu na kasashen musulmi a karo na farko a birnin Dakar ya bayyana cewa; wannan zama wani babban canji ne na ci gaba a cikin kungiyar hadin kan kasashen musulmi. Ya ci gaba da cewa bisa la'akari da cewa kasashen biyu mambobi ne na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, kuma wannan shi ne karo na farko da suka gudanar da irin wannan taro na addini na hadin gwiwa tsakaninsu, hakan manuniya ce ga babban sauyi a cikin kungiyar.


398660
captcha