Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Trade Chakra cewa; Kasar Malazia za ta dauki nauyin bakuncin taron mata na kasashen musulmi da za a gudanar wanda shi ne irinsa na farko. Bayanin ya ci gaba da cewa bisa la'akari da matsayin mata da kuma rawar da suke takawa a cikin dukkanin bangarori na rayuwar zamantakewa, bai kamata a bar su a baya ba wajen shirya gudanar da taruka masu amfani ga dukkanin al'umma. Bayanin ya ce hakika gudanar da wannan taro zai yi tasiri matuka wajen kara dankon dangantaka tsakanin mata na kasashen musulmi, tare da karfafa gwiwarsu wajen yin aiki tare domin ciyar da al'ummar musulmi gaba a dukkanin fuskoki, musamman ma a harkoki na tattalin arziki da zamantakewar jama'a.
399716