Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ma'akatar yada labarai ta kasar Afganistan cewa; An fara gudanar da wani taro kan matsayin mata a mahangar kur'ani mai tsarki a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan na hadin gwiwa tsakanin ma'aikatar kula da harkokin mata ta kasar Afganistan da kuma cibiyar kula da al'adun muslunci ta kasar Iran. Wannan dai shi ne karo na farko da ake gudanar da irin wannan taro a matsayi na yanki, wanda yake samun halartar mata likitoci da masana kan harkokin zamantakewa daga kasashen yankin, musamman ma daga kasashen Iran da kuma kasar ta Afganistan mai masafkin baki. Ana tattauna batutuwa masu matukar muhimmanci mata musulmi su sansu domin kyautata zamantakewarsu.
401011