IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Dora Wa Isra'ila Alhakin Kai Hari Kan Farararen Hular Gaza

15:09 - May 07, 2009
Lambar Labari: 1775195
Bangaren kasa da kasa: Kwamitin majalisar dinkin duniya da ke gudanar da bincike kan hare-haren kare dangi da Isra'ila ta kai kan al'ummar Gaza a farkon shekarar nan, ya dora alhakin kai hari a kan fararen hula da suka fake a cikin gine-ginen majalisar dinkin duniya da ke Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Islam online cewa; Kwamitin majalisar dinkin duniya da ke gudanar da bincike kan hare-haren kare dangi da Isra'ila ta kai kan al'ummar Gaza a farkon shekarar nan, ya dora alhakin kai hari a kan fararen hula da suka fake a cikin gine-ginen majalisar dinkin duniya da ke Gaza. Rahoton ya ambaci lokutan da jiragen yakin Isra'ila suka kai hare-hare kan fararen hula a sansanonin majalisar dinkin duniya da ke yankuna daban-daban na Gaza, da kuma adadin mutane fararen hula da suka rasa rayukansu sakamakon haka, akasarin wadanda suka mutu sakamakon hakan kananan yara ne da mata. Rahoton ya kara da cewa dukkanin hare-hare babu wanda aka kai kan kuskure, duk akan ganganci ne da sunan yaki da mayakan Hamas.

400743




captcha