IQNA

An Daga Taron Tattaunawa Addinai Zuwa Makonni Uku Masu Zuwa

15:24 - May 16, 2009
Lambar Labari: 1778971
Bangaren kasa da kasa: An dage gudanar da taron nan na tattaunawa tsakanin mabiya addinai da aka shirya gudanarwa a cikin makon nan har zuwa cikin watan gobe.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran APS cewa; An dage gudanar da taron nan na tattaunawa tsakanin mabiya addinai da aka shirya gudanarwa a cikin makon nan har zuwa cikin watan gobe. Wannan taron dai asusun tallafawa kanan yara da mata na UNESCO ne ya shirya gudanar da wannan zaman taro a birnin Dakar na kasar Senegal, da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi addinai da mabiyansu da kuma hanyoyin da za a bi wajen kara dankon alaka tsakanin mabiya addinai tare da kara kusanto da fahimtarsu, ta yadda za su zauna lafiya da juna. Daga cikin kasashen da za su halarci wannan zaman taro kuwa har da Jamhuriyar Benin, Ivory Coast, Gambia, Guinea Bissau, Nigeria Ghna Mali da kuma Senegal mai masafkin baki.


405381



captcha