IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Rayuwar Musulmi A Kasashen Duniya

15:24 - May 16, 2009
Lambar Labari: 1778972
Bangaren kasa da kasa: A yau za a fara gudanar da wani zaman taro a birnin Rebat na kasar Morocco, dangane d ayadda musulmi suke rayuwa a kasashen duniya daban-daban, da kuma sanin irin matsalolin da suke fuskanta da kuma dalilan da suke jawo hakan.
Kmafanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran dir group cewa; A yau za a fara gudanar da wani zaman taro a birnin Rebat na kasar Morocco, dangane d ayadda musulmi suke rayuwa a kasashen duniya daban-daban, da kuma sanin irin matsalolin da suke fuskanta da kuma dalilan da suke jawo hakan. Rahoton ya ci gaba da cewa cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Morocco ce ta dauki nauyin shirya gudanar da wannan taro, babbar manufar gudanar da zaman taron na yini biyu kuwa ita ce sani halin da musulmi suke ciki a ko'in cikin fadin duniya, da kuma yadda suke gudanar da harkokinsu na addini, a cikin kangi ko cikin walwala, da kuma ci gaba ko matsaloli da suke fuskanta, domin sanin hanyoyin da za a wajen taimaka musu.

405400



captcha