IQNA

16:06 - May 23, 2009
Lambar Labari: 1780498
Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da tarukan makon kur'ani a dukkanin garuruwan palastinu daga ranar Litinin, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani ta palastinu wato Alfurkan ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamafanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Bakr cewa; An fara gudanar da tarukan makon kur'ani a dukkanin garuruwan palastinu daga ranar Litinin, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani ta palastinu wato Alfurkan ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa. Wadannan taruka ana gudanar da su domin girmama kur'ani mai tsarki, wannan ne ma ya sa ake kiran makon da makon girmama kur'ani. Shugaban cibiyar da ke kula da shirya irin wadannan taruka a dukkanin garuruwan palastinu ya fadi cewa, babbar manufar gudanar da irin wadananan taruka dai ita ce samar da wani yanayi na fadakarwa dangane da muhimmancin da ke tattare da komawa zuwa ga kur'ani mai tsarki da koyarwarsa, wanda hakan ita kadai ce hanya ta samun nasara a dukkanin lamurran musulmi.

406893


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: