IQNA

15:46 - May 19, 2009
Lambar Labari: 1780556
Bangaren kasa da kasa; Kwamitin kula da harkokin mata da matasa ta fuskacin harkokin addinin a kasar Turkiya ya gudanar da wata gasar karatun kur'ani ta mata a birnin Esparta na kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga Medya cewa; Kwamitin kula da harkokin mata da matasa ta fuskacin harkokin addinin a kasar Turkiya ya gudanar da wata gasar karatun kur'ani ta mata a birnin Esparta na kasar. Mai kula da bangaren harkokin addini na mata a cikin kwamitin Aisha Dai ta bayyana cewa; mata da daman e suka halarci wannan gasar karatun kur'ani da aka gudanar ta yini guda a babban dakin taro da ke birnin Isparta na kasar Turkiya, wanda kuma zaman na jiya shi ne karshe a gasar wadda aka kwashe tsawon kwanaki ana gudanarwa, bayan da aka fitar da wadanda suka kai ga mataki na karshe, inda kuma a jiya ne suka kara da juna kuma aka kawo karshen gasar baki daya. Ta ce babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce karfafa gwiwar mata wajen shiga cikin harkokin kur'ani a fadin kasar don kar a bar su a baya.

407048

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: