IQNA

An Yi Zanga-zangar Nuna Kin Amincewa Da Wulakanta Kur'ani A Girka

16:05 - May 23, 2009
Lambar Labari: 1781979
Bangaren kasa da kasa: A jiya daruruwan mabiya addinin musulunci da ke birnin Athen na kasar Girka suka gudanar da wata zanga-zangar nuna kin amincewa da wulakanta kur'ani da wani dan sandan gwamnatin kasar ya yi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Reauters cewa; A jiya daruruwan mabiya addinin musulunci da ke birnin Athen na kasar Girka suka gudanar da wata zanga-zangar nuna kin amincewa da wulakanta kur'ani da wani dan sandan gwamnatin kasar ya yi. Shugaban gamayyar kungiyoyin musulmi na kasar Girka Na'im Qandur ya bayyana cewa, a ranar Laraba da ta gabata ce 'yan sanda suka kai wani samame a wani dakin cin abinci na wasu musulmi a birnin Athen, inda suka dauki wani kur'ani mallakin wani musulmi day a zo cin abinci a wurin suka keta shi a gaban jama'a kuma suka sa kafa suka taka shi, lamarin day a harzuka mabiya addinin musulunci da ke birnin.

409036






captcha