IQNA

Za A Fara Wani Shiri Na Safkar Kur'ani A Kullum Rana A Washington

16:34 - May 26, 2009
Lambar Labari: 1783477
Bangaren kasa da kasa: Cibiyar kula da harkokin ilimin addinin musulunci da ke birnin Washington na kasar Amurka, za ta fara gudanar da wani shiri da take da shi na safke kur'ani a kullum rana har tsawon wata guda, domin tunawa da zagayowar lokacin shahadar Fatimat Zahra AS.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na musulmin kasar Amurka cewa; Cibiyar kula da harkokin ilimin addinin musulunci da ke birnin Washington na kasar Amurka, za ta fara gudanar da wani shiri da take da shi na safke kur'ani a kullum rana har tsawon wata guda, domin tunawa da zagayowar lokacin shahadar Fatimat Zahra AS. Bayanin ya ce kofa a bude take ga dukkanin musulmi da suke zaune a birnin Washington da suke son shiga cikin wannan safka da su yi rijistar sunayensu, bangaren da ke kula da rijistar sunayen mutanen shi ne zai bayyana lokaci da kuma wurin da za a gudanar da wannan safka.

410785


captcha