IQNA

An Kawo Karshen Gasar Karatun Kur'ani A Kasar Qatar

15:47 - May 27, 2009
Lambar Labari: 1783989
Bangaren kasa da kasa: An kawo karshen gasar harda da karatun kur'ani ta kasa da aka gudanar a fadin kasar Qatar, wadda daliban makaratun sakandare suka gudanar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alraya cewa; An kawo karshen gasar harda da karatun kur'ani ta kasa da aka gudanar a fadin kasar Qatar, wadda daliban makaratun sakandare suka gudanar. Rahoton ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo na shida ake gudanar da irin wannan gasar kur'ani ta kasa baki daya da cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasar ke shiryawa. Shugaban cibiyar sheikh Taisir Khalid ya bayyana cewa; babbar manufar shirya irin wannan gasa ita ce karfafa gwiwar yara da kuma matasa kan rungumar kur'ani mai tsarki, kama daga bangaren harda da karatu har zuwa sanin ilmominsa tare da yin koyi da koyarwarsa kamar yadda Allah madaukakin sarki yake umurtarmu, ya ce ya zuwa yanzu an samu gagarumar nasara ta wannan fuska.

411281


captcha