IQNA

Ana Hankoron Haddasa Rikici Tsakanin Mahukuntan Saudiyya Da 'Yan Shi'a

12:19 - June 01, 2009
Lambar Labari: 1785501
Bangaren kasa da kasa: Daya daga cikin malaman mabiya mazhabar shi'a na kasar saudiyya kuma limamin juma'a na garin khabar da ke gabacin Saudiyya Sayyid Bakir Nasir ya bayyana cewa; masu tsattsuran ra'ayin wahabiyanci na hankoron haddasa fitina tsakanin mahukuntan saudiyya da kuma mabiya mazhabar shi'a na kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga gidan talabijin na Rasid cewa; Daya daga cikin malaman mabiya mazhabar shi'a na kasar saudiyya kuma limamin juma'a na garin khabar da ke gabacin Saudiyya Sayyid Bakir Nasir ya bayyana cewa; masu tsattsuran ra'ayin wahabiyanci na hankoron haddasa fitina tsakanin mahukuntan saudiyya da kuma mabiya mazhabar shi'a na kasar. Shaihin malamin ya bayyana hakan ne a cikin wani bayani day a fitar jiya, inda ya bayyana cewa; wasu daga cikin masu tsattsuran ra'ayin wahabiyanci suna tsokanar mabiya mazhabar shi'a ta hanyoyi daban-daban domin su mayar da martini saia danganta lamarin kai tsaye da mabiya mazhabar shi'a na kasar, daga cikin kuwa hard a tunzura mahukuntan wajen rufe masallatai da wuraren gudanar da harkokin ilimi da ibada na 'yan shi'a a Saudiyya.

413070

captcha