Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da taro kan harkokin banki a musulunci a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa, wanda yariman birnin Dubai Hamdan bin Muhammad bin Rashid Al Maktum ke jagorantar gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran WAM cewa; An fara gudanar da taro kan harkokin banki a musulunci a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa, wanda yariman birnin Dubai Hamdan bin Muhammad bin Rashid Al Maktum ke jagorantar gudanarwa. Rahoton ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da wannan taro dai ita ce yin dubi kan matsalolin da harkokin banki ke fuskanta yanzu haka a duniya, wanda kuma hakan yak an shafi kasashen musulmi kai tsaye, wanda kuma hakan ya samo asali ne daga matsalolin tattalin arziki da yanzu haka suka addabi duniya. Zaman dai zai dubi ne dangane da yadda ya kamata harkokin kudi su gudana a bankuna a mahanga ta musulunci.
414275