IQNA

Kwamitin Kananan Yara Larabawa Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Yaran Gaza

22:18 - June 06, 2009
Lambar Labari: 1787854
Bangaren kasa da kasa: Kwamitin kananan yara larabawa da ked a mazauni a birnin Alkahira na kasar Masar, ya yi kira da a kare hakkokin kananan yara da ke Gaza, da suka samu kansu cikin halin kaka ni ka yi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana cewa; Kwamitin kananan yara larabawa da ked a mazauni a birnin Alkahira na kasar Masar, ya yi kira da a kare hakkokin kananan yara da ke Gaza, da suka samu kansu cikin halin kaka ni ka yi. Kwamitin ya bukaci da a bayyana sakamakon zaman da aka gudanar a cikin shekara ta 2002 dangane da hakkokin kananan yara palastinawa da kuma yadda za a kare hakkokinsu. Kwamitin ya ce muhimmin lamari shi ne aiwatar da abin da ak cimmawa a aikace ba wai kawai tara takardu da ke dauke da kudurorin da ba ayi aiki da sub a. Zaman kwamitin na gaba za a gudanar da shi ne a cikin watan Janairun sabuwar shekarar miladiyya a birnin Jeneva na kasar Switzerland.

416362





captcha