IQNA

Gwamnatin Musulunci Dole Ta Ginu Kan Manufar Addinin Musulunci Na Asali

16:11 - June 07, 2009
Lambar Labari: 1788211
Bangaren kasa da kasa: Juyin juya halin musulunci a Iran ya tabbatar da cewa ci gaban gwagwarmayar annabawa ne, wanda Imam Khomeini ya aiwatar a aikace, kuma ya jagoranta bisa manufa ta addini.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Islam info cewa; daya daga cikin wadanda suka halarci taron tunawa da marigayi Imam Khomeini da aka gudanar a birnin Tehran, Dombia Ibarahim babban editan jaridar cewa; Juyin juya halin musulunci a Iran ya tabbatar da cewa ci gaban gwagwarmayar annabawa ne, wanda Imam Khomeini ya aiwatar a aikace, kuma ya jagoranta bisa manufa ta addini. Ya ce Daya daga cikin siffofin da Imam Khomeini mu'assasin juyin juya halin musulunci a Iran ita ce rashin tsoron makiyansa, tare da fuskantarsu ba tare da wani shayi ba, tare da dogaro da Allah madaukakin sarki. Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar juma'a a gaban dubban masallata a lokacin da yake gabatar hudubar sallar juma'a. Ya ce dogar da Allah shi ne babban sirrin duk wata nasara da Imam Khomeini ya samu a cikin gwagwarmayarsa, tun daga lokacin da yake gwagwarmaya har zuwa samun nasarar juyin juya halin musulunci a Iran.


416407

captcha